ABNA24 : ‘Yan tawayen na yunkurin shiga Bangui babban birnin kasar, wanda hakan babbar barazana ne cewar MDD, tare da bukatar kara yawan dakarun MDD, dake kasar.
Manyan kungiyoyin ‘yan tawayen da suka hade a wani kawance mai suna CPC, na rike da ikon kashi biyu cikin uku na kasar dake fama da yakin basasa na kusan shekaru 8.
‘Yan tawayen dai sun saka kafar wando guda da gwamnatin kasar ne gabanin zaben shugaban kasar na watan Disamba da ya gabata.
342/